Rashin wadatattun kayan aiki da rashin samun albashi akan lokaci na daga cikin jerin matsalolin da likitocin karkara ke matukar fama da su, a kan wanannan lamarin ne dai kungiyarsu ta Synasat ke ganin alama ce da ke nuni cewa mahukuntan Jamhuriyar Nijar ba su damu da kananan asibitocin kasar ba.
Abin da ke bai wa wasu kungiyoyin na daban damar cin albasa da bakin ‘ya'yanta kamar yadda sakataren kungiyar a reshen Say da Torodi Awal Yakuba ya gayawa manema labarai.
Yanzu haka zama likita a karkara wani abu ne mai cike da hadari saboda haka kungiyar Synasat ke jan hankalin hukumomin kasar akan bukatar baiwa magoya bayanta kulawar da ta dace.
Sannan sun kosa da abinda su ka kira da rikon sakainar kashin da ake yi wa likitoci ‘yan kwantiragi ya sa su ka fara barazanar shiga yajin aiki muddin aka ci gaba da tafiya a haka.
Ga Sule Mummuni Barma da cikakken rahoton:
Facebook Forum