Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitoci Sun Shiga Yajin Aiki A Najeriya


Likitoci a bakin aiki a Najeriya
Likitoci a bakin aiki a Najeriya

Likitocin suna kira ne da a ceto Dr. Ganiyat Popoola wacce ‘yan bindiga suka yi garkuwa da ita a Kaduna sama da watannin takwas da suka gabata.

Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa a Najeriya ta shiga aikin kwanaki bakwai a matsayin gargadi ga hukumomin kasar kan wata mambar da 'yan bindiga suka yi garkuwa da ita.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Shugaban Kungiyar Dele Abdullahi ya ce yajin aikin zai fara daga ranar 26 ga watan Agustan 2024.

Likitocin suna kira ne da a ceto Dr. Ganiyat Popoola wacce ‘yan bindiga suka yi garkuwa da ita a Kaduna sama da watannin takwas da suka gabata.

“An cimma wannan matsaya ce a taron gaggawa da shugabannin kungiyar suka yi. Yajin aikin na kwanaki bakwai ne a matsayin gargadi.” In ji Abdullahi.

A ‘yan makonnin da suka wuce kungiyar ta yi zanga-zangar lumana a dukkan asibitocin da ke sassan kasar don neman a kubutar da Dr. Popoola.

Dr. Ganiyat, rajistira ce a Sashen kula da lafiyar ido da ke Kaduna.

An kuma sace ta ne tun watanni takwas da suka gabata tare da mijinta da wani dan uwanta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG