Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Libya: Wani Hari Ya Hallaka Bakin Hauren Afirka Da Dama


Akalla mutum 40 mafi aksarinsu bakin haure daga nahiyar Afrika sun rasa rayukansu, kana wasu 80 sun jikkata a wani harin sama da aka kai a wata cibiya da ake tsare da bakin haure a kusa da Tripoli, kamar yadda rahotanni suka ruwaito.

Karamin Sakataran ma’aikatar harkokin cikin gida na kasar ta Libyan ya ce, adadin mutanen da suka mutu yana da yawa, amma masu ayyukan ceto na ci gaba gudanar da ayyukansu.

Kimanin mutum 200 ne suke cikin Cibiyar wacce ke Gundumar da ake kira Tajoura da ke wajen babban birnin na Tripoli.

An kwashe watanni ana gwabza fada a kokarin karbe ikon birnin Tripoli, tsakanin gwamnatin Libya da kasashen duniya suka amince da ita, da dakarun Libyan National Army da ke goyon bayan Janar Khalifa Haftar, amma babu wata alama da ke nuna cewa za a sasanta lamarin.

Su dai dakarun hamayya a kasar ta Libya sun tsame hannunsu daga wannan hari na sama, wanda aka kai da yammacin jiya Talata, inda suka dora laifin akan dakarun da ke marawa gwamnati baya.

Facebook Forum

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG