Jami’ai a kasar Libiya sun ce fadan da aka gwabza tsakanin wasu kungiyoyin ‘yan bindiga masu dauke da manyan makamai a babban birnin kasar ya firgita mazauna yankin tare da kashe mutane kusan dozin daya, tashin hankali na baya bayan nan a wannan kasa ta arewacin Afirka da mafi yawanta babu doka da oda.
Jami’an sun kara da cewa, fadan da aka shafe sa’o’i ana gwabzawa, wanda ya hada da manyan makamai, ya faru ne a ranar Juma’a a unguwar Tajoura da ke gabashin birnin Tripoli ko Turabulus, tsakanin mayakan Rahba al-Duruae, karkashin jagorancin jagoran yaki Bashir Khalfallah, wanda aka fi sani da al-Baqrah, da kuma wata kungiyar ‘yan bindiga ta al-Shahida Sabriya.
Sashen Motocin Daukar Marasa Lafiya da Ayyukan Gaggawa na Ma’aikatar Lafiyar kasar ya ce akalla mutane 9 ne suka mutu, sannan wasu 16 suka jikkata a rikicin da aka kwashe sa’o’i ana yi.
Rikicin ya samo asali ne daga yunkurin kashe al-Baqra da aka yi a ranar Juma’a, wanda mayakansa suka daura alhakinssa kan al-Shahida Sabriya, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito.
Khaled al-Meshry, wanda shi ne sabon shugaban majalisar gudanarwar kasar da ke yammacin kasar, ya yi Allah wadai da yunkurin kisan gillar da aka yi, tare da yin kira da a gudanar da bincike domin hukunta wadanda suka aikata laifin.
Bangarorin biyu da ke gaba da juna suna kawance da gwamnati Firai minista Abdul Hamid Dbeibah.
Sai dai kakinta bai amsa bukatar yin magana kan lamarin ba.
Tashin hankalin dai ya nuna raunin kasar Libiya bayan boren da aka yi a shekarar 2011, da ya rikide ya koma yakin basasa, wanda ya kifar da gwamnatin Moammar Gadhafi da ya dade yana mulki kama karya.
Yayin da ake cikin rikicin, mayakan sun samu karuwar dukiya da iko, musamman a Tripoli da yammacin kasar.
AP
Dandalin Mu Tattauna