Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babbar Kotun Kano Ta Bada Umurnin Dakatar Da Binciken Gwamna Ganduje


KANO: Dr. Abdullahi Umar Ganduje gwamnan Kano
KANO: Dr. Abdullahi Umar Ganduje gwamnan Kano

Da alama, aikin binciken da majalisar dokokin Kano ke yi kan zargin karbar na goro daga hannun ‘yan kwangila na dala miliyan biyar a kan gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya samu koma baya, bayan da babbar kotun jihar ta bada umurnin dakatar binciken har sai ta kammala sauraren karar gabanta.

Kungiyar lauyoyi masu rajin demokaradiyya a Najeriya wato Lawyers for Sustainable Democracy in Nigeria, ita ce ta shigar da karar a makon jiya, tana mai ikirin cewa majalisar ta karya sassan kundin tsarin mulki tare da yin azababi wajen daukar gabarin wannan aiki na bincikar zargin rashawar dala miliyan biyar daga hannun ‘yan kwamgila.

Zaman kotun na ranar Litini karkashin jagorancin Justice A.T Badamasi ya ta’allaka ne a kan tababar fassarar umurni da kotun ta bayar ne wadda ke hani ga majalisar ta dakatar da binciken zuewa lokacin sauraron shari’ar.

Ita dai majalisar a baya tace odar kotun ba ta fito karara ta hana aikin binciken ba, a don haka bata fahimtar cewa, a dakatar da aikin binciken faifen bidiyon.

Alkalin kotun mai shari’a AT Badamasi ya nanata bukatar dakatar da binciken har sai kotun ta kammala sauraron gundarin shari’ar.

To amma a yayin tafka mahawara, lauyan majalisar dokokin Barriter Mohammed Waziri ya fadawa kotu cewa, dama kwamitin bai ci gaba da aikin binciken ba.

Barriter Muhammed Zubair dake zaman shugaban kungiyar lauyoyin data gurfanar da majalisar gaban kotun ya bayyana jin dadinsa a kan yanda ba a samu jayayya a kan karar da suka shigarwa kotun a kan dakatar da binciken.

Ga dai cikakken rahoton da wakilin mu a Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko mana:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG