Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AL-Shabab Tace Zata Hari Magoya Bayan Sabon Shugaban Somalia


 Mohamed Abdullahi Farmajo
Mohamed Abdullahi Farmajo

Wani babban jami’in kungiyar AL-Shabab yace, 'Yan kungiyar masu tsatstsauran ra’yin addinin Islama basa goyon bayan zaben Mohamed Abdullahi Farmajo a matsayin shugaban kasar Somaliya

Hassan Yaqub Ali, Wanda yake daya daga cikin manyan shuwagabannin Al-Shabab kuma gwamnan masu tsatstsauran ra’ayin a lardin Galgudud yayi barazanar kungiyar zata kai hari kan duk wata kabila ko duk wanda ya goyi bayan sabon shugaban kasar.

Ya fada a jawabin da aka saka a kafar yada labaran kungiyar ta al-shabab a daren asabar in da yace, “Zamu yake shi a tsawon shekaru hudu da zai yi yana mulki.”

Yan majalisar Somaliya ne suka zabi Farmajo a ranar 8 ga watan Fabrairu a zaben da da yawan al’ummar Somaliya suka yi murna da shi.

Da yawa daga cikin wadanda suka yi murna da zaben nasa sun yaba da irin aikin da yayi na tsahon wata bakwai a matsayin firaminista daga shekarar 2010 zuwa 2011. A wancan lokacin ya biya albashin ma’aikatan gwamnati da kuma na sojojin kasar. Sannan ya taka muhimmiyar rawa wajen hada kan sojojin Somaliya da na Dakarun tarayyar Afirka wajen yakin da ya fatattaki yan kungiyar Alshabab daga kusa da fadar gwamnatin kasar.

Da alamun manyan jami’an Al-shabab sun damu da farin jinin da Farmajo yake dashi, in da suke cewa Shugaban ba mai kishin kasa bane.

Da sukai martini akan murna da sowa da akai a fadin kasar, Ali yace masu yin murnar kungiyoyin sakaine suka biya su kudi.

Ali ya kara da cewa “ duk wanda yake da fasfo na wata kasa to bamai kishin kasa bane”.

Farmajo dai yana da shiadar zama dan kasa biyu ne Somaliya da Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG