Mutane da ke fama da tabin kwakwalwa suna kuma fargaban fuskantar tsangwama idan suka fita fili suka bayyana suna fama da wannan lalura.Wata kungiya a Najeriya da ake kira MANI a takaice, tana samar da damar da mutane za su iya samun jinya ba tare da fargaban tsangwama ko wariya ba.