ABUJA, NIGERIA - A shirin 'Lafiya Uwar Jiki' na wannan makon mun tattauna ne da Dr. Muslim Bello Katagum da ke asibitin Ni'ima a Azare, jihar Bauchi akan ciwon gabobi ko Amosanin gabobi kamar yadda wasu ke kiran cutar, wani nau'i ne na ciwon gabobi mai tsanani da ke addabar gabobi dan adam, yakan zo da kunburi a gabar da ke ciwon, kuma cutar tana aukuwa ne yayin da jiki ke fitar da sinadarin Uric Acid da yawa ko fiye da kima.
Sau tari cutar tafi kama gabar babban yatsar kafa duk da cewa takan iya kama sauran gabobi na jiki da suka hada da gwiwa.
Saurari cikakken shirin da Hauwa Umar ya gabatar:
Dandalin Mu Tattauna