Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Abuja, bayan kusan mako biyu a Ingila inda yayi jinyar kunne.
"Lafiya ta kalau. Kun ganni ina kallon fareti.," shugaban na Najeriya ya gayawa gungun manema labarai a tashar jiragen sama. "Ina da karfi. Idan ma kana jin zaka yi kokawa ne da ni bismillah," aka ji shugaban yana fada da Hausa.
Dan shekaru 73 da haifuwa, shugaba Buhari ya tafi ingila ne ranar 6 ga watan nan, domin ya ga kwararrun likitoci ta fuskar jinyar kunne da da hanci da kuma makogwaro, a zaman mataki na "sanin tabbas," kamar yadda hadiman shugaban suka fada.
Da farko an shirya shugaban zai koma Najeriya ne ranar Alhamis data shige, amma jinkirta komawar, sai ta janyo fargaba gameda lafiyarsa, a dai dai lokacinda kasar take fama da matsalolin barazanar tsaro daga 'yan binidgar Boko Haram, da kuma matsanancin tallalin arziki.