Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamred Dauda: Matasa Sun Zama Motar Alfa A Siyasar Najeriya


Kwamred Dauda Muhammad Gombe
Kwamred Dauda Muhammad Gombe

Shirin mu na matasa da siyasa a yau mun yada zango ne a garin Damaturu babban birnin jihar Yobe, inda muka tattauna da wani matashi da ke wakiltar Kungiyar Matasan Arewa.

Ita dai kungiyar ta matasan Arewa mai burin kawo cigaban kasa, wato North East Youth Initiative for Development.

Kwamred Dauda Muhammad Gombe, ya ce matasa na Allah wadai da hali na Sanata Elisha Abbo, na keta hakkin wata mace duk da cewar Sanatan ya bada hakuri, ya kara da cewa matasa sun nesantar da kan su da wannan Sanata, sakamakon kasancewar ya wuce shekarun da za’a kira shi matashi.

Ya ce har yanzu da saura matasa mussaman ma wajen damawa da matasa a siyasa, kuma hakan zai faru ne da zarar an canza tsare-tsaren yadda ake tafiyar da demokradiyya da sauran mulki a Najeriya.

A baya an dama da matasa, amma a wannan zango duk da irin gudunmuwar da matasa suka bayar wajen kada kuri’un su maza da mata, ana zaton a mukaman za’a nada ya kasance kaso 40 zuwa 60, amma haka bai faru ba, duk da irin gwagwarmayar da suka yi.

Kwamred Dauda ya ce sabanin haka matasa zasu yi zaton anyi musu butulci, sakamakon ba’a yaba da gudunmuwar su ba. Ya kara da cewa sanya matasa a mukaman, wata dama ce da cigaba ga mulkin Najeriya, domin ana sanya su a kan hanya ne kafin lokacin da zasu fara daukar manyan mukaman mulkin kasar baki daya.

Samun matasa a madafan iko zai bada damar cigaban al'umma sannan daukaka ce a kasar Najeriya a idon duniya.

A saurari cikakken rahoton hirar su da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:10:53 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG