Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamishinan 'Yan Sandan Birnin Tarayya Ya Lashi Takobin Kamo Wadanda Suka Hallaka Abubakar Ibrahim


Yau ranar laraba kwamishinan ‘yan sanadan babban birnin tarayyar Najeriya Abuja Mr Wilson Inalegwu ya lashi takobin zakulo wadanda suke da hannu a rasuwar shugaban tsare-tsaren hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya NFF Ibrahim Abubakar.

Abubakar ya rasu ne a yau laraba a gidan sa dake Abuja a sakamakon harbinsa da wasu wadanda ba a san ko su wanene ba suka yi.

Kwamishinan ‘yan sanda Inalwgwu ya isa gidan marigayin da misalign karfe 8:20 na safiya, bayan sun gama binciken harabar gidan, jami’an tsaron sun bayyana cewa zasu yi duk abinda zasu yi domin gano wadanda suka aikata wannan aika aika.

Yau rana ce da aka wayi gari cike da hawaye da bakin cikin rasuwar daya daga cikin jaororin na hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriyar, manyan jami’an hukumar karkashin jagorancin babban sakatare janar din hukumar Dr Mohammed Sanusi sun halarci jana’izar marigayin da aka gudanar a jahar Kaduna.

Shugaban hukumar ta NFF Amaju Pinnck ya dauki lokaci mai tsawo kafin ya dawo cikin hayyacin sa a yayin da ya sami labarin rasuwar Abubakar ta wayar tarho, ya kuma mika gaisuwar sag a hukumar da ‘yan uwa da abokan arziki baki daya.

Ministan matasa da wasanni Solomon Dalong ya kasance ministan matasa da wasanni na farko da ya fara kai gaisuwar ta’aziyyar sa a ofishin hukumar a yayin da ya isa Glass House tare da sakaren din-din-din Mr Christian Ohaa, dukkan su sun sa hannu a rajistar jerin masu mika gaisuwar ta’aziyyar mamaci.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG