Rahotanni da dumidumin su sun bayyana rasuwar shugaban tsare tsaren hukumar kwallon kafa ta Najeriya Mr Ibrahim Abubukar a gidan sa dake Gwarinfa, kusa da Kado Estate da ke babban birnin Abuja.
Ibrahim Abubakar mai shekaru 43 da haihuwa ya rasu ne a sakamakon kisan gilla da wasu ‘yan fashi suka yi masa a yau laraba.
A cewar babban sakataren hukumar Dr Mohammed Sanusi wanda ke cike da da fargaba da damuwa, mamacin wanda ake kira Ibro cikin wasa ya bar ofishinsa jiya talata da yamma cike da fara’a, ya kuma kara da cewa lallai hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta yi babban rashin ma’aikaci mai kwazo da kuma kishin aikin sa.
Ibrahim Abubakar ya fara aiki da hukumar a shekarar 2007, kuma za’a yi jana’izar sa yau a jahar kaduna kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Ya rasu ya bar mata da ‘ya’ya maza guda uku, Allah ya jikanshi da rahama Amin.