Ma’aikatar tsaron kasar Tunisia tace mutane 46 ‘yan ci rani ne suka mutu bayan da kwale-kwalen da suke ciki ya nutse a kudancin gabar tekun kasar, haka kuma mutane 67 ne jami’an dake gadin gabar tekun suka ceto, jiya Lahadi.
Sanarwan da ma’aikatar tsaron tafitar tace ana ci gaba da wannan aikin ceton, Kuma ‘yan ci ranin wasun su ‘yan kasar ta Tunisia dama sauran wasu ‘yan kasashe.
A wani al’amari na daban kuma an samu mutuwar mutane 9 ciki ko harda yara 6 da suka mutu a jiya Lahadi bayan da karamin jirgin ruwan da suke ciki mai dauke da mutane 15 ya nutse a gabar tekun kudancin Turkiyya dake gundumar Antalya, kamar yadda jamiaan dake gadin gabar Tekun na kasar Turkiyya suka fitar da sanarwa.
Rage kwararan ‘yan ci rani a kasar Italiya shine daya daga cikin manufofin jamiyyar yaki da zuwa ci rani na kasar Italiya, wanda shugabanta shine Matteo Salvini da aka rantsad a ranar jumaan data gabata a matsayin ministan harkokin cikin gida
Facebook Forum