Kwalajojin kimiya da fasaha nada matukar tasiri wajen koyar da dalibai ayyukan hannu na dogaro da kai ba sai sun dogara da ayyukan gwamnati ba.
A can baya kungiyoyin malaman kwalajojin da sauran ma'aikata sun sha tafiya yajin aiki saboda rashin kular da suka ce hukumomin Najeriya na nuna masu.
Dr Abubakar Abdul Zukogi shugaban kwalajin kimiya da fasaha na gwamnatin tarayya dake Bidda ya yi karin bayani. Yace idan sun yaye dalibansu suna iya samar ma kansu aiki ba sai sun jira aikin gwamnati ba. Saboda haka yace suna rokon gwamnati ta mayar da hankali akan ilimin kimiya da fasaha domin idan babushi da wuya kasa ta cigaba.
Ya kwatanta yadda gwamnati ta dauki jami'o'i. Misali idan an ba jami'a daya nera miliyan dari da kyar a ba kwalajin kimiya da fasaha miliyan talatin. Yace banbancin ya yi yawa. Yace rokonsu a nan shi ne a karawa kwalajojin kimiya da fasaha kudin da ake basu.
A kan daliban da su da jami'o'i ke yayewa yace kada a duba takardar shaidar kare karatu kawai a basu aiki kana a basu albashi bisa ga iyawarsu da kwarewa. Yace haka ake yi koina a duniya.
Ga karin bayani.