Taron kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen jihohin Arewaci 19 da Abuja sun dau alwashin wayar da kan mabiya, muhimmancin hakuri, da gudanar da bincike cikin adalci kafin daukar wani mataki a yayin da duk aka samu wani akasi.
Kungiyar ta cimma wannan kuduri ne a wani gagarumin taro da ya samu halartar matasan 'CAN' daga dukkan sassan Arewacin Najeriya. Shugaban kungiyar Mai-Bushara Musa Misal, ya nesanta addini da daukar doka a hannu, ya kuma ce zaman lafiya ya fi zama dan Sarki.
Taron ya samu halartar matasa mata, da ma dattawa da su ka taya matasan fitar da bayanan, ciki kuwa har da Pasto Paul Gwaza da sakataren gwamnatin Najeriya Boss Mustapha.
Tattaunawa tsakanin kungiyoyin mabiya addinnan Kirista da Musulmai na da muhimmanci, domin barin hukuma ta zama mai daukar hukunci ba mutane masu banbancin akida ba.
Ga rahoto cikin sauti daga wakilin muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum