Akalla kungiyoyin kwallon kafa a nahiyar Turai shida ne suka fara nuna sha’awarsu ta sayen mai tsaron baya na kungiyar Chelsea Antonio Rudiger.
A karshen wannan kakar wasa kwantiragin Rudiger zai kare a kungiyar ta “The Blues” mai taka leda a gasar Premier League ta Ingila.
Sai dai rahotanni na cewa har yanzu wakilan Rudiger dan shekara 28 da mahukuntan kungiyar ta Chelsea ba su fara tattaunawa ba.
Ko da yake, akwai wani dan kwarya-kwaryan zama da aka yi a tsakanin bangarorin biyu amma Rudiger ya ce zai bar “kofar zabinsa a bude.”
Akwai alamu da ke nuna cewa mai yiwuwa Rudiger ya ci gaba da zamansa a Stamford Bridge.
Shafin wasanni na Sky Sports ya ruwaito cewa daga cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan har da Bayern Munich.
Ko da yake, Rudiger ya nuna godiyarsa ga kungiyar ta Bundesliga da ta nuna sha’awarta akansa, amma ya ce yana jin dadin zamansa a Chelsea.
Rudiger wanda dan asalin kasar Jamus ne, ya ce ba zai yi hanzarin yanke hukunci kan makomarsa ba, saboda “muhimmin lamari ne da ya shafi rayuwarsa ta kwallo.”