Bayanan da aka samu daga ma’aikatun lafiya na kauyen Dei Dei sun nuna akwai cutar gudawa da yawa a kauyen, wanda yasa suka kama kokari domin kiyaye yaduwar wannan cutar.
Yayinda take bayani ga ‘yan jarida, shugabar kungiyar, Mrs. Maureen Machie tace wata manufar kungiyar Rotary itace taimakon jama’a su shawo kan matsalolinsu da ya hada da lafiya kamar lafiyar iyaye mata da ‘ya’ya yara.
Machie ta kara da cewa, kungiyar taje kauyen ne ta fadakar da jama’a saboda da yawan cutar gudawa a kauyen, kan yadda zasu lura da kansu, musamman kan cutar gudawa, yadda take yaduwa da kuma hanyar maganinta.
Tayi bayanin cewa domin rashin isashen kudi ba zasu iya zuwa dukan kauyukan dake birnin tarayya ba.
Dr. Inibon Ekong tace sun sami ruhoton yawancin cututtukan da ruwa mara kyau yake kawowa musamman gudawa, kwalara da atini kuma kungiyar ta gane bisa ga bayanan cewa masu fama da cutukan sun yi yawa saboda haka kungiyar take hada hannu da ‘yan bautar kasa a kauyen domin fadakarwa da kuma kokarin shawo kan yaduwar cutar gudawa.
Kayayyakin da aka rarraba a kauyen sun hada da kayan wanka, pampers, Sabulai, maganin tsabtace ruwa da kiyaye shi.