Kungiyar ta ECOWAS ta ce ta ga irin halin da wadannan mutane suke ciki musamman a arewacin Najeriya, dan haka ne ta dau wannan matakin taimaka musu da zai rage musu radadin talauci da matsalar karancin abinci da suke fama da shi a wurare daban daban.
Darekta a ma’aikatar samar da agaji ta gwamnatin tarayya, Grema Ali Alhaji da ya mika kayan abincin ga gwamnatin jihar Borno a madadin kungiyar ECOWAS, ya ce jihohin da za su amfana da kayan abincin sun hada da, Borno, Yobe, Bauchi, Kogi, Katsina, da kuma Zamfara, kana kowace jiha zata samu motocin biyar cike da kayan abinci.
Grema ya kara da cewa wannan taimako ne ga 'yan gudun hijira dake zaune a sansanonin da ba su da abinci, kana ya ce sun fada wa hukumar SEMA da kuma gwamnatin jihar Borno cewa wannan gudunmuwa ce ta ECOWAS ga masu gudun hijira kadai.
Hajiya Yaba Yakolo shugabar hukumar samar da agajin gaggawa ta jihar Borno da ta amshi kayan abinci a madadin gwamnatin Borno, ta ce suna turawa jihohi makwabta a jamhuriyar Nijer kayan abincin, kana ta yi kira ga sauran kungiyoyi su bada gudunmuwa ga mutanen da rikicin ‘yan ta’adda ya shafe su.
Ta ce jihar Borno dake da kashi 80 cikin 100 na ‘yan gudun hijira miliyan biyu a arewa maso gabashin Najeriya, bata zaci wannan lamari zai dauki tsawon lokaci kamar yadda ake gani a yanzu ba. Amma a-kwana-a-tashi sai aka kwashe sama da shekaru goma ana fama da wannan matsala ta ‘yan gudun hijira. Ta ce kada a gaji dasu, a ci gaba da kawo musu dauki.
Yanzu haka gwamnatin jihar Bornon na ta shirye shiryen maida ‘yan gudun hijira garuruwansu na asali ko kuma wasu garuruwa dake da dan dama-dama don ci gaba da rayuwarsu kamar yanda yake a baya.
Ga dai rahoton Haruna Dauda Biu daga Maiguguri: