An kashe Isak Mohammed Ibrahim ne, lokacinda bam din da aka boye cikin motarsa ya tashi. Wani dan Majalisar mai suna Mohammed Abdi yaji rauni a harin.
Ofishin Prime Ministan kasar ya tabbatar da wannan labari. Kungiyar 'yan yakin sa kai ta Al Shabab tace ita keda alhakin kai harin.
Cikin dai 'yan shekarun da suka shige, kungiyar tayi hasarar yawancin yankunan data mamaye, domin sojojin kungiyar kasashen Afrika dana gwamnatin Somaliya sun kwace su.
To amma duk da haka yan yakin sa kan, sunci gaba da kai hare hare jefi jefi.
A watan Fabrairu ma, mutane goma sha bakwai aka kashe, lokacinda mayakan kungiyar Al Shabab suka kutsa fadar shugaban kasar. Shugaba Hassan Sheikh Mohammed baiji rauni a harin ba.