Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kulli Kurciyar Mulkin Taraba Tsakanin Sanata Jummai Da Gwamna Darius


Sanata A'isha Jummai Alhassan Daga Taraba
Sanata A'isha Jummai Alhassan Daga Taraba

Tun bayan gama zaben shekarar da ta gabata ta 2015 a Najeriya ne ake ta kai ruwa rana tsakanin jam'iyyar PDP da APC game da kowannensu na cewa su suka lashe zaben gwamnan jihara Taraba.

Wato tsakanin Darius Dickson Ishaku da Aisha Jummai Alhassan da suka nemi kujerar ta gwamna. To a baya wata kotu ta bawa ita Aisha Jummai din nasarar cewa a bata kujerarta don ita ta ci zabe.

To sai dai shi kuma Gwamna Ishaku bai yi kasa a gwiwa ba ya garzaya kotun daukaka kara don kalubalantar hukuncin shari'a da aka bata nasarar da ita. Cikin sa'ar da yayi kuwa sai aka sake cewa shi ya lashe zaben.

To amma har yanzu himma bata ga rago, domin kuwa tace tabbas zata daukaka kara zuwa kotun daga ita sai Allah ya isa. Sannan kuma ta tabbatar da yadda suke sa ran cewa Allah yana tare da su.

Kamar yadda shima Gwamna Darius yace Allah ne shima tare da shi yasa aka soke wancan hukuncin kotun ta baya da ta so ta cilla ta kan karagar mulkin jihar da cewa ita ta ci zaben jihar ta Taraba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:12 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG