Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kudin Aikin Hajji Ka Iya Kai N10m Sakamakon Kawo Karshen Tallafi Da NAHCON Ta Yi

Hajj House NAHCON, Abuja
Hajj House NAHCON, Abuja

Sanarwar da kakakin hukumar alhazan, Fatima Sanda Usara, ta fitar tace, a aikin hajjin badi, “maniyata daga jihohi ko ‘yan jirgin yawo ba zasu samu rangwame ba wajen samun kudaden musaya daga gwamnati.”

Hukumar Alhazan Najeriya (NAHCON) ta bayyana cewar gwamnatin kasar ba zata biya tallafi akan alhazan 2025 ba.

Sanarwar da kakakin hukumar alhazan, Fatima Sanda Usara, ta fitar tace, a aikin hajjin badi, “maniyata daga jihohi ko ‘yan jirgin yawo ba zasu samu rangwame ba wajen samun kudaden musaya daga gwamnati.”

Hakan na nufin idan har aka cigaba da sauyin dala akan n1, 650, kowane maniyaci zai biya kusan naira milyan 10 a matsayin kudin kujerar aikin hajji kwatankwacin akalla dala dubu 6.

A yayin da har yanzu nahcon bata sanarda kudin kujerar aikin hajjin badin ba, hukumomin alhazan jihohi sun bukaci maniyata su biya n8.5m a matsayin kafin alkalami kafin lokacin da za’a sanarda kudin kujerar.

Haka kuma sanarwar ta sanarda mayar wa kowane alhajin da ya sauke farali a 2023 da naira 64, 682 (kwatankwacin riyal din Saudiya 150).

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG