Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Daukaka Kara Ta Mayar Da Muhuyi Magaji Kan Mukaminsa

Magaji Muhuyi
Magaji Muhuyi

Hakan ya biyo bayan hukuncin da kotun mai alkalai 3, karkashin jagorancin Mai Shari’a Umaru Fadawu ta zartar, wanda ya bayyana dakatarwar da lamarin mai cutarwa kuma tauye hakkin Muhuyi Magaji ne na jin ba’asinsa.

Kotun daukaka kara ta Abuja ta rushe dakatarwar da aka yiwa shugaban hukumar yaki da almundahana ta Kano, Muhuyi Magaji daga kan mukaminsa.

Hakan ya biyo bayan hukuncin da kotun mai alkalai 3, karkashin jagorancin Mai Shari’a Umaru Fadawu ta zartar, wanda ya bayyana dakatarwar da lamarin mai cutarwa kuma tauye hakkin Muhuyi Magaji ne na jin ba’asinsa.

Da yake yanke hukuncin a yau Juma’a, Mai Shari’a Fadawu ya bayyana cewa, “dakatarwar da kotun da’ar ma’aikata ta yi muhuyi ba ta dace ba kuma ta sabawa tsarin jin ba’asin ko wane bangare. Kuma mun umarci a mika batun ga wani rukunin alkalan kotun da’ar ma’aikata na daban.”

A ranar 4 ga watan Afrilun 2023 aka dakatar da muhuyi magaji, sakamakon zarge-zargen aikata ba dai dai ba da kotun da’ar ma’aikatan ke yi masa.

Kotun da’ar ma’aikata, karkashin jagorancin Mai Shari’a Danladi Umar, ta umarci Gwamnan Kano, Abba Yusuf, da sakataren gwamnatin jihar su nada wanda zai jagoranci hukumar yaki da cin hancin a mataki na riko har sai an kammala sauraron karar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG