Kotun BradFord ta yanke ma tsohon dan wasan kungiyar Manchester City, da Sunderland, Adam Johnson hukuncin daurin shekaru shidda a gidan kaso a sakamakon samun sa da akayi da laifin anfani da wata yarinya ‘yar shekaru goma sha biyar da haihuwa da akayi a farkon wannan watan amma ya a jiya alhamis ya daukaka kara.
Kungiyar Sunderland ta dakatar da kwangilar ta da dan wasan mr Johnson a samakon samunsa da alaifin da aka yi, ta garzaya kotu domin kauce ma cecekucen kafofin sadarwa, kuma ta saurari bayanan wanda ake tuhumar wanda ta bayyana a matsayin wani abu mai nakasu a rayuwar yarinyar da kuma sha’anin karatunta.
Mai gabatar da karar ya bayyana yadda masu goyon bayan Johnson ke ci gaba da bata sunan yarinyar a shafukan yanar gizo.
Lauyan Mr Johnson Dr Philip wanda mai kula da lafiyar kwakwalwa ne yayi ikirarin cewa hankalin Johnson bai cika ba a irin shekarun sa, sakamakon tangardar da ya samu ta rashin habakar kwakwalwa a lokacin da yake tasowa.
Likitan dan wasan Dr Philip ya bayyana yadda Johnson ya kasa bada bayanan laifin da ya aikata saboda kunyar da yaji na aikata wannan danyen aiki.
A karshen yanke hukuncin sa, alkalin kotun mai shari’a Jonathan ya tashi inda ya ce ma Johnson “wannan dai laifin ka ne, kuma alhakin ya rataya akan ka”.
Alkalin ya kara da cewa “cikar ta shekaru goma sha biyar Kenan ka fara bata mata rayuwa domin kawai ka yi shi’awarta duk da cewa kasan shekarunta sha biyar da haihuwa kacal’.