Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Tsara Rayuwar Aure Da Aiki A lokaci Guda-Inji Jamila Mai Iyali


Jamila Mai Iyali
Jamila Mai Iyali

A shirinmu na wasu muhimman mata da suka taka muhimmiyar rawa a cikin alummarsu a yau mun sami zantawa da wata matashiya Mal Jamila Hamisu Mai Iyali mace mai kamar maza.

Malama Jamila dai ta ce tana kammala karatuntun ta na jami'a ta fara aiki , don haka tun farkon rayuwarta na zaman aure ta tsara shine bisa turban hada aiki da aure don haka ne ma bata san matsaolilin hada aiki da aure ba a cewarta da haka ta fara a matsayinta na matar aure.

Ta kara da cewa kasancewar ta samu miji mara damuwa kuma wanda ya fahimce ta a matsayin matarsa ne ma ya sa bata fuskantar kalubale da dama , duk kuwa a cewa ba'a rasawa, a cewarta lokaci yayi da mata zasu nemi ilimi ko na boko ko na adini muddin mace na bukatar samun rayuwa mai inganci, domin kuwa a wannan zamani duk macen da bata da ilimi an bata a baya.

Tana mai cewa duk matar da take da ilimi tarbiyar 'ya'ya zai zo mata da sauki kuma yaran zasu sami kyakkawan tarbiya dfomin duk abinda za'a yi za'ayi shine cikin ilimi.

ku biyo mu domin jin yadda hirar ta mu ta kasance.

XS
SM
MD
LG