Kamfanin man fetur a Najeriya, NNPC ya ce ya gano dumbin arzikin iskar gas dankare a karkashin kasa a yankin kananan hukumomin Kanam da Wase a jihar Filato.
Shugaban kula da aikin tonon man fetur a kamfanin NNPC, Abdullahi Bomai ya ce sun gano sinadarin Hydrocarbon wanda ya ce kara gudanar da bincike zai bayyana irin albarkatun da ke karkashin kasa.
Mai martaba Sarkin Kanam, Alhaji Mu’azu Muhammadu ya ce gudanar da aikin hakar mai da iskar gas zai kawo ci gaba ga yankin.
Mr. Tersoo Agah da ke zama malami a sashen binciken albarkatun kasa a jami’ar Jos ya ce wannan zai kara martabar da Najeriya ke da shi na zama kan gaba a bangaren samar da man fetur a Afirka.
Mataimakin gwamnan jihar Filato, Farfesa Sonni Tyoden ya ce a shirye gwamnati take ta tallafa wajen samun nasarar aikin.
Saurara karin bayani a sauti:
Facebook Forum