Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukuma Za Ta Biya Wani Mutumin Florida Diyyar Dala Miliyan 14 Saboda Daure Shi Shekaru 37 Bisa Kisan Da Bai Aikata Ba


Robert DuBoise
Robert DuBoise

Robert DuBoise ya shafe shekaru 37 a gidan yarin Florida saboda laifin fyade da kisan kai a 1983 da bai aikata ba. Yanzu jihar Florida za ta biya shi dala miliyan 14 a matsayin diyya na tsawon shekarun da yake daure.

An dai yanke wa Duboise wadda ke shekaru 18 a lokacin da laifin ya afku hukuncin kisa da farko saboda kashe Barbara Grams mai shekaru 19. Ko da yake daga baya an rage hukuncin daurinsa zuwa rai da rai a gidan yari, sai dai a shekarar 2018 - tare da taimakon kungiyar da ke kare wadanda ake kyautata zaron basu aikata laifin da aka daure su a kai ba, masu shigar da karar suka amince su sake waiwayar karar.

Gwajin DNA da a lokacin babu shi a shekarar 1980, ya nuna alamun wasu mutane biyu ne ke da hannu a kisan, wanda ya kai ga sakin DuBoise daga kurkuku a 2020. Ba da dadewa ba, DuBoise ya kai karar birnin Tampa da ke Jihar Florida, da jami'an 'yan sanda wadanda suka binciki lamarin da kuma likitan hakora wanda ya shaida cewa hakoransa sun yi daidai da alamar cizon wadda aka kashen.

An dai daidaita karar ne a ranar 11 ga watan Janairu amma Majalisar birnin Tampa ta kada kuri’ar amincewa a ranar Alhamis din da ta gabata tare da ba DuBoise dala miliyan 14 a hukumance, wanda ya kai shekaru 59 a yanzu. Mambobin Majalisar sun ce kudin shine mafi karancin abin da birnin zai iya yi masa.

"Wannan babban kuskure ne," in ji dan Majalisa Luis Viera. "Ina fata da kuma addu'ar cewa zai dan sami sa’ida daga wannan biyan diyyar."

DuBoise da kamfanin lauyoyinsa za su samu dala miliyan 9 a bana, dala miliyan 3 a shekara mai zuwa da dala miliyan 2 a shekarar 2026, a cewar takardun.

An dai yi lalata ne da Barbara inda aka kuma yi mata duka aka kashe ta a watan Agusta 1983 yayin da ta ke komowa gida bayan ta tashi daga shagon cin abinci da take aiki a Tampa.

~AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG