Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Sa A Tsare Malam Idris Abdulaziz A Gidan Gyaran Hali


Dr. Idris Abdulaziz
Dr. Idris Abdulaziz

Kotu a jihar Bauchin Najeriya ta sa a tsare wani fitaccen Shehin Malami kuma limamin masallacin Juma'a na Dutsen Tanshi da ke jihar Bauchi Dr. Idris Abdulaziz a gidan gyaran hali bisa zarginsa da aikata kalaman batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W)

An kama shi bisa zargin shi da yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad a lokacin da ya ke huduba a watan Ramadan.

Rahotanni sun nuna cewa jama’a da dama daga cikin al’ummar Musulmi a Jihar Bauchi ba su ji dadin kalaman malamin ba, wadanda suka kwatanta a matsayin abin Allah wadai da ban takaici.

Sakamakon haka, an tuhume shi da laifin tunzura jama’a da cin mutuncin ra’ayin addini, wadanda laifi ne a karkashin dokokin Najeriya.

Lamarin dai ya haifar da ce-ce-ku-ce a yankin. Wasu masu goyon bayan limamin sun ce yana amfani da ‘yancin fadar albarkacin baki ne, yayin da wasu kuma suka yi Allah-wadai da kalaman da ake zarginsa da yin kira da a hukunta shi.

Ana ci gaba da shari'ar, kuma har yanzu limamin yana tsare.

Lauyan Limamin Barista Umar Hassan ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya shaidawa manema labarai cewa wanda yake karewa ya gurfana a gaban wata kotun Majistare.

Alkalin ya ki amincewa da belinsa, sannan ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi har sai ranar Talata mai zuwa.

Masu lura da harkokin addini da na shari’a a Najeriya sun sanya ido sosai kuma suna ci gaba da bibiyar lamarin.

Yusuf Aminu

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG