Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Ce Za a Iya Fara Aiwatar Da Dokar Hana Shiga Amurka


Harabar kotun kolin Amurka inda 'yan jarida suka yi dafifi domin jiran hukumcin kotun akan dokar Donald Trump
Harabar kotun kolin Amurka inda 'yan jarida suka yi dafifi domin jiran hukumcin kotun akan dokar Donald Trump

Bayan an dade ana kai komo akan dokar Donald Trump ta hana 'yan asalin wasu kasashen Musulmai shida shiga Amurka, yanzu kotun kolin kasar ta amince da cewa wani bangaren dokar ya fara aiki.

Kotun kolin Amurka ta amince ta saurari karar da shugaba Donald Trump ya shigar kan dokar da ya yi ta hana shiga Amurkan, inda da farko kotun ta yanke hukuncin cewa wani bangaren dokar zai iya fara aiki.

Dokar hana shiga Amurkan wacce aka yi wa kwaskwarima, ta shafi wasu kasashe shida Musulmai suke da rinjaye matuka har na tsawon kwanaki 90.

Sannan dokar za ta hana ‘yan gudun hijrar kasashen shiga Amurka har na tsawon kwanaki 120.

Umurnin na Trump har ila yau ya bayyana cewa, daukan wannan mataki ya na da muhimmanci domin zai taimaka wajen kare kasar daga hare-haren ta'adanci daga waje.

Gabanin wannan hukuncin na kotun kolin, wasu kotunan tarayya biyu na daban, sun dakatar da aiwatar da dokar, daya daga jihar Hawaii daya kuma daga jihar Maryland.

Dukkanin hukunce-hukunce da kotunan biyu suka yanke sun samu goyon bayan kotunan daukaka kara.

Kasashen da dokar za ta shafa sun hada da Libya da Iran da Somalia da Sudan da Syria da kuma Yemen.

Sai dai alkalan kotun kolin, sun ce aiwatar da dokar ba za ta shafi mutanen kasashen ba wadanda ke da alaka ta gaskiya da wani dan Amurka ko kuma wata cibiya.

Kotun ta ba da misalin irin rukunin wadannan mutane a matsayin wadanda ke da alaka ta dangantaka, da dalibai, da wadanda jami’oi suka basu guraben karatu da ma’aikata da kuma wadanda suka samu tayin aiki a Amurka.

A jiya Litinin, shugaba Trump ya bayyana hukuncin wannan kotu a matsayin “babbar nasara.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG