Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Ce A Tsare Matar Da Ake Zargi Da Kashe Kishiyarta A Gidan Kaso


Wani zaman kotu a Najeriya.
Wani zaman kotu a Najeriya.

Rahotanni sun ce kotun ta tura su gidan yarin ne don su yi zaman jira, gabanin ta karbi shawarwari daga ma’aikatar shari’ah ta jihar Nejan.

Kotun Majistire da ke garin Minna a jihar Nejan Najeriya, ta sa a tsare matar da ake tuhuma da kashe kishiyarta a gidan yari.

Alkalin kotun, Mai Shari’ah Nasiru Ma’azu, ya tura Amina Aliyu gidan kaso ne, bayan da ta gurfana a gaban kotu a ranar Laraba tare da wasu mata uku da ake zargin sun taimaka mata wajen aikata wannan laifi.

Rahotanni sun ce kotun ta tura su gidan yarin ne don su yi zaman jira, gabanin ta karbi shawarwari daga ma’aikatar shari’ah ta jihar Nejan.

A makon da ya gabata ne aka zargi Amina da laifin bugawa kishiyarta Fatima Ibrahim tabarya a ka, a lokacin da suka mata taron dangi da wasu ‘yan uwanta uku, lamarin da ya yi sanadin mutuwarta.

Karin bayani akan: Fatima Ibrahim, Minna, Nigeria, da Najeriya.

Bayanai sun yi nuni da cewa, sun kuma kunnawa gidan Fatima wuta bayan da suka nakasa ta, a wani kokari da suka yi na ganin sun nuna kamar gobara ce ta yi sanadin mutuwarta.

Marigayiya Fatima Ibrahim
Marigayiya Fatima Ibrahim

Gidan marigayiyar da uwargidan daban-daban ne kamar yadda bincike ya nuna.

‘Yan sanda ne dai suka gabatar da Amina tare da wasu mata 3 da ake zargin sun taimaka mata wajen aikata wannan danyen aiki, kamar yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar Nejan Alhaji Adamu Usman ya ce.

“Tun da aka kamo su, suna hannanmu, bayan mun gama abin da muke yi, mun kai su kotu a yau (Laraba).” In ji Usman.

Ya kara da cewa sun kai Amina kotu ne inda suke tuhumarta da laifin kisan kai.

“Abin da ake tuhumarta sun hada da laifukan da suka shafi kisan kai ne.” Ya kara da cewa.

Shugabar Hukumar kare hakkin yara da mata a jihar Nejan, Barrista Maryam Kolo ta ce sun gamsu da tuhume-tuhumen da ‘yan sanda suka yi ma wadanda ake zargin.

“Mun je wajen ne (kotu,) saboda mu tabbatar kotu ta yi abin da ya kamata, mun kuma ji dadi ‘yan sanda sun yi abin da ya kamata, don sun yi bincike mai tsanani, kafin suka kai su gaban kotu.” In ji Kolo.

Saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari daga Minna:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00


XS
SM
MD
LG