Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiya Ta Saki Wasu 'Yan Fafutikar Kare 'Yancin Bil Adama da Suke Fuskantar Shari'a


'Yan fafutikar kare 'yancin Bil Adama a Turkiya
'Yan fafutikar kare 'yancin Bil Adama a Turkiya

A wani yunkuri na bazata hukumomin Turkiya sun saki 'yan fafutikar kare 'yancin Bil Adama da suke fuskantar shari'a bisa zargin aikata ta'addanci wadanda aka sake jiya Laraba din sun hada da daraktan Amnesty International na yankin Turkiya Idil Eser

Kasar Turkiyya ta saki wasu ‘yan fafutukar neman ‘yancin Bil Adama guda takwas, a lokacin da ake jiran sakamakon shari’ar da ake musu kan zargin aikata ta’addanci.

Cikin mutanen da aka saka a jiya Laraba, har da daraktan kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International shiyyar Turkiyya Idil Eser , tare kuma da wani dan Jamus guda da kuma wani dan kasar‘dan asalin kasar Switzerland daya.

An dai kamasu ne a watan Yuli lokacin da suka halarci wani taron karawa juna sani kan tsaro a kafafen sadarwa a tsibirin Buyukada. Aka kuma ci gaba da tsare su tun daga lokacin.

Jimlar ‘yan fafutukar 11 ne ake tuhuma da zargin suna mu’amula da mayakan Kurdawa masu ra’ayin rikau, ana kuma zarginsu da zama mambobin kungiyar da babban malamin nan Fetullah Gulen ke jagoranta wanda kuma yanzu haka ke zaman buya a Amurka.

Turkiyya ta ce Malam Gulen da magoya bayansa sune da alhakin yunkurin yujin mulkin da bai sami nasara ba a shekarar da ta gabata, wanda malam Gulen ya musanta hakan.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG