'Yan kasar Sipaniya sun kada kuri jiya Lahadi, a zaben kasar na hudu a cikin shekaru hudu.
Ana sa ran Firaiminista Pedro Sanchez na jam’iyyar gurguzu ya lashe zaben, kamar yadda ta faru a zaben da ya gabata.
A jawabinsa wajen wani gagarumin yakin neman zabe, Firaiministan yace, "a yau kuri’a ce za ta yi aiki wajen zaben shugabancin Sipaniya a gobe. Babban muhimmin al’amari shine yin kira ga ‘yan kasar Sipaniya da su yi zabe, da kuma karfafa dimokaradiyyar kasar ta hanyar zaben"
Yakin neman zaben da ya kai da zaben na ranar Lahadi, ya maida hankali ne akan yunkurin samun ballewa da ‘yancin kasar Catalonia, da kuma fargabar habakar jam’iyyar Vox.
A zaben da ya gabata, jam’iyyar shugaban na Spaniya ta kasa lashe isassun kuri’un da za su ba ta damar kafa tsayayyar gwamnatin.
Jam’iyyar Vox ce dai ya kamata ta kasance abokiyar hadakar jam’iyyar ‘yan gurguzu da ke mulki, to amma babu jituwa a tsakaninsu, bayan zaman tattaunawa da dama da ba su yi nasara ba, biyo bayan zaben watan Afrilu, da kuma rashin babbar damar samun kuri’un da za su kafa gwamnatin tare.
Facebook Forum