Aliyu Adam Muhammad King A, mawakin hip hop ne, kuma dalibine a makarantar sakandare ya kuma bayyana ya ce kasancewarsa a matsayin dalibi, ba zai hana shi yin waka ba. A cewarsa, sha’awace, ta sa ya fara, kuma yana baiwa kowanne lokacinsa .
Ya bayyana cewa waka wata hanya ce ta isar da sako da kuma nishadantarwa a lokaci guda. Ya ce waka, baiwa ce.
Yana mai jan hankali mawaka masu tasowa, da su daina nuna dagawa da rashin da’a, tare da yi musu biyayya.
King A, ya ce ko da ya fara waka, ya fuskanci matsaloli da dama. Ya ce soyayya ce ta sa ya fara waka. Soyayya da wata budurwar da aka hana shi ne ya sa ya fara waka.
Ya ce bayan fitar da wakarsa ta farko, mahaifinsa bai ji dadin hakan ba domin kuwa sai da ya shafe kwanaki uku baya fitowa, kasancewar an hanashi fita daga gida.
King A, ya kara da cewa a wannan lokaci mahaifinsa ya dauki waka a matsayin rashin ji, da rashin da’a.
Facebook Forum