WASHINGTON, DC - A watannin baya-bayan nan jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya ta fuskanci tashin hankalin ‘yan bindiga masu kisa da garkuwa da mutane don neman kudin fansa, lamarin da ya jefa al’umar yankin cikin yanayin zullumi.
Wakilin Muryar Amurka Lamido Abubakar, ya tattauna da wasu ‘yan kasuwar da suka bayyana cewa babban kalubalen da suke fuskanta a harkokin kasuwancinsu shi ne zaman fargaba saboda rashin tsaro.
Bayan hauhawar farashen kayayyaki da ke shafar hada-hadar kasuwanci, ‘yan kasuwar sun koka da cewa suna biyan kudin haraji sosai kafin kayansu su isa kasuwa, kasancewar galibi kayan gwari daga arewacin Najeriya ake kaisu yankin.
Saurari cikakken shirin da Lamido Abubakar ya gabatar.