Adadin wadanda suka kamu da cutar Coronavirus a jirgin ruwan dakon jiragen yakin saman Amurka mai suna USS Theodore Roosevelt da ke Guam, sai dada karuwa yake.
Hakan na faruwa ne a yayin da shi kansa babban jami’in da ya kori kaftin din jirgin ya yi murabus a jiya Talata.
Jami’an sojin ruwan Amurka sun gaya wa Muryar Amurka cewa, 230 daga cikin sojojin ruwan sun kamu da cutar.
Ya zuwa safiyar Talata, yawan sojojin ya kai kashi 15% na daukacin dakarun Amurka da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a fadin duniya.
A makon jiya kwamandan jirgin ruwan, Kyaftin Brett Crozier, ya rubuta wata takardar nuna damuwa ga na gaba da shi, ya na mai kiransu da su yi abin da ya kira, “daukar gagarumin mataki” don kauce ma mace-mace a cikin jirgin sanadiyyar cutar Coronavirus.
Mukaddashin Sakataren Sojin Ruwan Amurka Thomas Modly, wanda ya kori kaftin din jirgin Crozier ranar Alhamis, shi ma ya ajiye aiki a radar Talata, bisa radin kansa, a cewar Sakataren Tsaron Amurka Mark Esper.
Facebook Forum