A kasar Kamaru 'yan gudun hijira daga kasar Najeriya sun kai kimanin dubu hamsin da suke jibge a garin Minawawo a jihar Arewa Mai Nisa wadanda kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya da na Tarayyar Turai da kuma kasar Kamaru suke kula dasu.
Ana ba 'yan gudun hijiran ruwan sha, abinci, magunguna tare da ba yaransu kanana ilimin zamani. Rikicin Boko Haram ne ya daidaita 'yan Najeriya suka yi gudun hijira zuwa kasar Kamaru
Alhaji Madu, ma'aikaci a ma'aikatar harkokin cikin gidan Kamaru yace 'yan gudun hijiran Najeriya dake kasar Kamaru sun dade inda suke amma hukumomin kasashen biyu sun zauna sun tattauna sun kuma ga lokaci yayi da zasu mayarda mutanen zuwa Najeriya.
Inji jami'in gwamnatin Kamaru kasar Najeriya ta amince 'yan kasarta su koma gida amma har yanzu Kamaru na jiran Najeriya ta tabbatar hakan ya faru. Da can Kamaru ta mayarda wasu 'yan Najeriya din amma akan dubu hamsin dake Minawawo sai sun samu tabbaci daga Najeriya kuma ta aiko da motocin da zasu kwashesu.
Ita ma Kamaru tace tana da mutanenta da dama a Najeriya kuma tana son Najeriya ta mayar dasu Kamaru.
Abdullahi Laser wani dan gudun hijira wanda ya kwashe sama da shekaru biyu a Kamaru yace babu wani abun alfaharin da ya fi su koma kasarsu saboda suna zama a Kamaru ne kara zube. Yana fatan gwamnati tayi kokari a maidasu saboda wai sun gaji.
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kasar Kamaru ta mayarwa bangaren Ingishin kasar yanar gizo gizo da ruwan sha da wutar lantarki kuma ta umurni hukumomin kasar ta Kamaru su mutunta mutuncin Bil'Adama.
Ga rahoron Garba Awal da karin bayani.