Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Da COVID-19 Ta Fi Mamaya a Duniya


Ma'aikatan lafiya dauke da gawar wani da cutar coronavirus ta halaka a birnin New York da ke Amurka. REUT.
Ma'aikatan lafiya dauke da gawar wani da cutar coronavirus ta halaka a birnin New York da ke Amurka. REUT.

Annobar coronavirus ta kama sama da mutum miliyan daya kana ta kashe fiye da 60,000 a duk fadin duniya.

Mafi aksarin wadannan alkaluma da aka fitar a ranar Asabar sun fi ta’azzara ne a nahiyar turai da Amurka.

Kasar Spaniya na da sama da mutum 124,700 da suka kamu da cutar sannan sama da 11,700 sun mutu.

Hakan ya sa hukumomin kasar suke tunanin tsawaita dokar hana fita daga ranar 15 ga watan nan na Afrilu har zuwa ranar 26.

A ranar Asabar Firai Ministan kasar Pedro Sanchez ya ce zai nemi majalisar kasar ta tsawaita dokar a karo na biyu.

A baya, ya nemi majalisar ta tsaiwata dokar zuwa ranar 11 ga watan na Afrilu.

A Birtaniya kuwa, Ma’aikatar Shari’ar kasar ta ce za ta saki dubban fursunoni cikin makonni masu zuwa, a wani mataki na yakar cutar.

Mutum 4,300 suka mutu a Birtaniya bayan da hukumomin suka bayyana samun mutuwar mutum 708 cikin dare guda.

A Faransa kuwa, dakarun kasar sun fara jigilar marasa lafiya zuwa asibitoci da ke sassan kasar domin kaucewa yaduwar cutar.

Sama da mutum 6,500 suka mutu a kasar, sannan wasu 83,000 sun harbu da cutar.

A halin da ake ciki Amurka ce cibiyar annobar a duk fadin duniya inda take da sama da mutum 278,500 da suka kamu da cutar.

Sai dai ana zargin gwamnatin kasar da jan kafa wajen yin amfani da mataki na bai-daya domin yaki da cutar.

Rahotanni na nuni da cewa shugaba Donald Trump ya umurci kowacce jiha da ji da kanta wajen shawo kan cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG