Tun a makon jiya ne dai kasar ta Turkiyya ta kaddamar da hari kan kungiyar ISIS da kuma dakarun Kurdawan da ke samun goyon bayan Amurka, wadanda gwamnatin Turkiyya ke daukarsu a matsayin masu alaka da 'yan tawayen kungiyar Ma'aikatan Yankin Kurdawa.
Fada tsakanin Turkiyya da Kurdawan ya dada rikita al'amarin da tun dama ke a rikici a Siriya, inda gwamnatin ta rinka samun goyon baya daga Iran da Rasha da 'yan Hezbollah da ke Lebanon a yayin da kuma Amurka da sauran manyan kasashen Yamma ke goyon bayan 'yan tawayen Siriya din.
"Za mu ci gaba da daukar matakan soji har sai barazanar da kan iyakokinmu da 'yan kasarmu ke fuskanta ta zo karsh," a cewar Firaministan Turkiyya Binali Yildrim ga manema labarai.
Tunda farko a jiya Laraba, kasar Iran ta yi kiran da Turkiyya ta gaggauta kawo karshen matakan soji da ta ke daukawa a arewacin Siriya, ta na mai cewa cegaba da kasancewar sojojin Turkiyya a wurin zai dada zafafa tashin hankalin ne kawai.
Hare-haren na Turkiyya ya yi nasarar fatattakar mayakan ISIS daga garin Jarablus, kafin su ka shiga rigima daga bangaren kudu da Kurdawa, wadanda su kansu sun taimaka wajen sake kwato garin Manbij.
Wani babban janar din sojin Amurka ya fadi ranar Talata cewa Kurdawa sun sake ketarowa baya zuwa gabashin kogin Euphrates, nesa daga Manbij, a wani al'amarin da Amurka ke fatan zai kawo karshen rigimar.