Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hannun Agogo Ya Dawo Baya Game Da Shari'a Dan Wasan Amurka OJ Simpson


Dan Wasan Kwallon Kafar Zari Rugar Amurka OJ Simpson
Dan Wasan Kwallon Kafar Zari Rugar Amurka OJ Simpson

Wukar da aka samu shekarun baya a wani rukunin gidajen da gidan tsohon dan kwallon kafar Amurka a birnin Los Angeles wato OJ Simpson yake, ana kyautata zaton yayi amfani da ita ne a wajen aikata kisan kai guda 2 a shekarar 1994 da ta shude ciki har da kashe matarsa.

Kamar shafin Intenet din TMZ da ya fara bada labarin yace, wani leburan gine-gine ne ya tono wukar akan iyakar rukunin gidajen a lokacin da ake rushe su don kwaskwarima. Wukar dai wani dan sanda mutumin ya mikawa, wanda shi kuma a ranar baya bakin aiki don haka ya ajiyeta bai kaiwa hukuma ba.

Sai bayan ritayar Wannan dan sanda ne ya sanar da abokinsa cewa ana son ya kai wukar ga hukuma. Kasancewar wanda ya tsinci wukar ya kai maganar gaba na wukar da ya tono tun a shekarar 1998.

An bayyana wukar da cewa irin karamar nan ce da ake ninketa, sannan ta yi matukar tsatsa. Wannan dai na zuwa ne bayan sa ran da ake yiwa Mista OJ na yafiya kila a shekarar 2017 ta badi.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG