A jamhuriyar Nijar yau shugaba Mahamadou Issoufou, ya jagoranci bukin dasa tubalin farkon soma aiyukan shimfida bututun mai daga matatar Zinder zuwa garin Torodi dake yankin Tilabery. a wani yunkurin fitarda man kasar zuwa kasuwanin yammacin Afirka. lamarin da zai bada damar samarda aikin yi ga miliyoyon matasa.
Bututun wanda za a shinfida da ya kai tsawon kilomit 1,070, wata hanya ce ta fitarda man da jamhuriyar Nijar ke tacewa a Zinder, don isar da shi kasuwanin kasashen Mali, Burkina da Faso. Lamarin da zai bada damar rage cinkoson ababen hawa, da ma takaita hatsura akan hanyoyin zirga zirga.
Dala biliyan $1 na Amurka kasar China za ta kashe domin wannan aiki da ake saran kammalawa a tsawon shekaru 2.
Shugaban kamfanin CN Pipe Line Company na cewa aikin shinfida bututun zai kunshi wasu cibiyoyin kan hanya a kalla 10, ya yinda za a yi jona domin isarda tatacen man zuwa Tahoua.
Wakilin muryar Amurka a yamai Sule Mumuni Barma ya aiko mana karin bayani.
Facebook Forum