Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Misira Na Bukatar Daukar Matakan Tsaro Masu Inganci


Kasar Misira tana bukatar daukar mataki mai inganci na shawo kan barazanar ta’adanci da ta ke fuskanta, kamar yadda wadansu kwararru kan ayyukan ta’addanci a Washington suka shaidawa Muryar Amurka.

Makon jiya, shugaban kasar Misira Abdel Fattah el-Sissi ya umarci jami’an tsaronsa su yi amfani da karfin soji wajen maido da “tsaro da zaman lafiya” a kasar dake yankin Sinai cikin watanni uku.

Umarnin yazo ne bayan kazamin harin da aka kai a masallacin Sufi watan da ya gabata da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane dari uku a kauyen al-Rawdah dake arewacin Sinai, hari mafi muni da kungiyar masu tsats-tsauran ra’ayin addinin Islama suka kai a tarihi. Daga cikin mutane dari uku da biyar da aka kashe, akwai kananan yara ishirin da bakwai,yayinda wadansu dari da ishirin da takwas kuma suka ji rauni.

Masu sharhi kan lamura sun ce harin da aka kai masallacin Sufiya manuniya ce ta rashin tasirin, matakin da gwamnati ta dauka na shawo kan ayyukan ta’addancin, kuma kasar na bukatar daukar kwakkwaran mataki a maimakon dibar wa’adin shawo kan ta’addancin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG