An dauki matakin sabunta kiddidigar ne bayan da aka samu tabbacin sake bulluwar cutar a asibitoci 3 a Mbandaka, wani gari mai kimamain mutane fiye da miliyan 1 a lardin Equateur dake arewa-maso-yammacin kasar.
Hukumar ta ce tana shirin aika masana 30 don su duba garin. Daman hukumomin sun riga sun aika da Alluran rigakafi 4,000 ga babban birnin kasar, Kinshasha.
An tabbatar da kamuwar mutum 44, da suka hada da wadanda ake zaton sun kamu da cutar tun da aka samu bulluwar cutar satin da ya wuce wanda ya hada da mutane 23 da suka mutu.
Mafi munin bulluwar cutar Ebola dai ya afku ne a shekarar 2014 inda mutane fiye da 11,000 suka rasa rayukansu a kasashen Guinea, Liberia da Saliyo, dukkansu a Afrika ta Yamma.
Facebook Forum