Mutane sun bayyana ra’ayoyinsu game da yadda suke kallon zaben da aka ce a sake na wasu kananan hukumomin jihar da a zaben baya da ya gabata aka sami tashe-tashen hankulan da dole aka soke zabukansu.
To an gudanar da zaben a kananan hukumomin ciki har da karamar hukumar Ijaw Kudu da itace dai din a yanzu ake jiran a ji sakamakon zaben. A baya din an yi rikice-rikice har da asarar rayuka. Wasu jama’ar Bayelsa din ma na ganin ya kamata a manta da ‘yan takarar da suke ja musu matsala.
Domin kuwa wani matashi ya bayyana cewa, ‘yan takarar guda biyu Silva na APC da Dickson na PDP da sun eke da ‘yan bindigar da ke tadawa jama’a hankali. Wata mata ma ‘yar kasuwa cewa ta yi suna bukatar canji a jihar yadda ya kamata.
Inda mafiya yawan wadanda suka yi maganar so suke su sami sabbin ‘yan takara masu martaba rayuka da dukiyar al’ummar jihar Bayelsa ba wadanda ke ja musu rikicin da a kullum sai an rasa rai ko asarar dukiya. Wakilinmu Lamido Abubakar Sakkwato ne ya aiko rahoton daga Bayelsa.