Zazzabin Lasa, wanda wani nau’in bera ke yadawa, na cigaba da haddasa mace-mace a sassan Najeriya. Na baya-bayan nan shi ne kashe mutane a kalla 16 da wani zazzabin da ake kyautata zaton na Lasa din ne ya yi a jahar Naija.
Ma’aikatar Lafiyar Jahar Naija, wadda ta tabbatar da mutuwar mutane 16 din, ta shiga fadakar da mutane game da illar cutar. Ta ce ta aike da samfurin cutar dakunan bincike don tabbatar ko ita ce ko kuma wata mai kama da ita ce.
Kwamishinan Lafiya na jahar Naija, Dokta Mustapha Jibrin ya shawarci mutane su tabbata beraye ba su fitsari ko kashi kan abincinsu ko kuma duk wani abubuwan da su ke mu’amala da su. Ya bayyana alamomin kamuwa da cutar ta Lasa.
Ga dai wakilinmu Mustapha Nasiru Batsari da cikakken rahoton: