Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kano: Hukumonin Kashe Gobara Sun Dangata Gobarar Gidan Mai Ga Rashin Kiyaye Ka'idoji


Yayin da Jami’an kiwon lafiya ke ci gaba da kula da fiye da mutane 70 da hadarin gobara ya ritsa da su a gidan sayar da man fetir na Al-ihsan dake kan titin Sharada a birnin Kano, hukumomin kashe gobara a jihar na danganta lamarin da rashin kiyaye ka’idoji daga bangaren mamallaka gidan man.

Yanzu haka dai wadanda wannan iftala’I ya afkawa a karshen mako na karbar magani a asibitin kwararru na Murtala dake tsakiyar Birnin Kano.

Duk da cewa, galibin mutanen da wannan waki’a ta fadawa na cikin mawuyacin hali, amma wasu daga cikin su na yin karfin hali, inda har-ma su kan yi magana da manema labarai inda suka ce garin kashe gobarar ne feshin man ya abka masu.

Yayin da gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyin yin magani ga wadannan mutane, hukumomin kwana-kwana a jihar sun yi tsokaci game da musabbabin wannan gobara. Alhaji Hassan Ahmed Mohammed, shine Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Kanon. Ya kuma ce rashin bin ka'idojin DPR ne ya ke janyo irin wadannan hatsarin.

Daga nan Alhaji Hassan Ahmed Mohammed ya shawarci masu gidan mai a jihar kan abin da ya kamata su yi da suka hada da tabbatar da cewa suna da kayan aikin kashe wuta a kowani lokaci kuma ana sabis dinsu akai-akai.

Saurari cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG