Kano, Nigeria —
Hukumar zaben kananan hukumomi a jihar Kano Najeriya ta ce zata gudanar da gwajin gano ta’ammali da ababen sanya maye ga dukkannin ‘yan takarar shugabancin kananan hukumomi da kansiloli a zaben da za a yi a watan gobe. Sai dai kasa da sa’o’i 24 da wannan furuci, fiye da mutane 300 masu muradin shiga takarar zaben suka kai kansu ofishin hukumar NDLEA na Kano domin yin gwajin. Wannan batu ya ja hankalin masu sharhi a jihar inda su ka yi tsokaci akan wannan batu.
A saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Dandalin Mu Tattauna