‘Yan sandan Nijeriya sun ce kananan ‘yan matan nan 32 masu juna biyu, na iya fuskantar tuhuma, bayan an zarge su da shirin sayar da jarirai, a wani tsarin safarar yara.
‘Yan sanda sun damke kananan ‘yan matan da wani likita mai wani dan asibita a jihar kudu maso gabashin Nijeriya ta Abia ran Asabar.
Kwamishinan ‘yan sanda Bala Hassan y ace akan aje ‘yan mata masu cikin ne cikin dan asibitin har sai sun haihu.
‘Yan sanda na zargin likitan da sayen jariran daga wurin ‘yan matan, sannan ya sayar da su kan dubban daloli ga ma’auratan dab a su da ‘ya’ya don kazamin riba.
‘Yan sandan sun ce akan bad a yan matan daga $160 zuwa $190, ta yadda farashin jarirai maza ya fi yawa.
Shugaban asibitin ya musanta zargin sayar da jiriran. Ya zake cewa asibitin mafaka ce ga kananan yan mata masu cikin da ba su bukata, kuma akan aje jariran ne wa masu sha’awar raya su.
Hukumomi na ma tsammanin akan sayi wasu daga cikin jariran ne, don a yi amfani da sassan jikinsu wajen tsafi.