Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boma Bomai Sun Tashi A Wata Ma'aikata A Maiduguri


Wata kasuwa a birnin Maiduguri,fadar jihar Borno.
Wata kasuwa a birnin Maiduguri,fadar jihar Borno.

Hukumomin Jihar Borno sun tabbatar da rahoton fashe fashe har biyu cikin daren jiya a unguwar Dokeri dake birnin Maiduguri,babban birnin jihar.

Boma Bomai Sun Tashi A Wata Ma'aikata A Maiduguri

A daren jiya laraba ce da misalin karfe bakwai d a rabi zuwa takwas na dare ne mazauna unguwar Dokeri suka ji karar fashe fashe biyu da ake kyautata zaton Bam a wata ma'aikatar gwamnati inda ake adana magunguna yaki da cututtuka masu yaduwa.

Mazauna unguwar sun gayawa wakilin sashen Hausa da ya ziyarci unguwar Alhamis din nan, cewa bayan sun ji karar fashe fashen suka fito waje sai suka ga wuta ta kama sosai a ma'aikatar da ake adana magungunan yaki da cututtuka masu yaduwa.

Wakilin Sashen Hausa yace lokacinda ya isa wurin hayaki yana ta tashi daga wutan,ga kuma garewanin motoci da wutar ta cinye.

Kantuna da suke kusa da ma'aikatar da gidajen zama suma wutar tayi musu barna.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG