Kamfanin Manhajar Twitter yace zai kara tsatsaura ka’idojin amfani da manhajar saboda ya dakile amfani da ita wajen cin zarafin mata.
Wannan sabon tsari za’a fara amfani dashi ba tare da bata lokaci ba sannan kuma zaa rufe shafin duk wani wanda aka kama yana aikata yada hotunan tsiraici a manhajar.
Kuma zaa ba mutane damar kai karar duk wani wanda suka ga yana watsa hotunan da basu dace ba a manhajar Twitter din wanda ada mutane basu da wannan damar amma yanzu zasu samu.
Kamfanin Manhajar Twitter din ya kara da cewa yanzu haka ma sun fitar da wata sabuwar doka ta hana yada kalaman batanci da kuma amfanin da alamu nuna batanaci.
Shugaban kamfanin manhajar Twitter Jack Dorsey shine ya bayyana wannan sabon sauye sauyen a shafin shi na twitter ranar juma’a inda yayi kira ga masu amfani da shafin da su daina kalaman da bai kamata ba a manhajar.
Facebook Forum