Fitaccen kamfanin fasahar nan mai suna Microsoft zai dakatar yin na’urar wasannin bidiyo ta Xbox, bayan kwashe shekaru goma yana cin kasuwarta.
Babban jami’in dake kula da sashen kera na’urar Xbox Phil Spencer, yace duk da yake na’urar ta shiga zukatan duk ma’aikatan dake kera ta, gaskiyar magana anan itace ba zasu iya ci gaba da kera na’urar ba.
Sai dai Microsoft zai ci gaba da sayar da sauran Xbox din da yake da su, kuma zai ci gaba da taimakon mutanen da ke da na’urar har sai sun kare. Mutanen dake da Xbox ba zasu sami matsala ba wajen yin wasanninsu babu abinda zai canza.
An fara sayar da Xbox ta farko a watan Nuwambar shekara ta 2005, an kuma sauya mata kamanni har sau biyu inda cikin shekara ta 2010 akayi Xbox 360 da kuma Xbox 260 Elite a shekara ta 2013. Tun shekara ta 2013 da kamfanin ya fitar da sanarwar ya sayar da Xbox har Miliyan 7.2, bai kara fitar da bayanan cinikinsa ba.
Wannan labarin ya fito ne cikin sanarwar da kamfanin Microsoft ya fitar. Masana sunyi harsashen kamfanin ya gazane a dalilin yadda kasuwar Kwamfuta tayi kasa, amma kamfanin ya kara samun kwarin gwiwa da sauran kayan da yake kerawa.