KANO, NIGERIA - Sai dai wasu daga cikin maniyyata umarar daga Najeriya na cikin rudani da yanayin rashin tabbas.
Yau dai an shiga kwana na biyar kenan daruruwan maniyyata umarar da suka sayi tikitin kamfanin jirgin sama na Azman suna cikin rudani saboda rashin jirgin da zai yi jigilarsu zuwa kasa mai tsarki.
Alhaji Mohd Turare gwamna daga jihar Yobe ya zargi kamfanin na Azman da rashin dattako, kamar yadda wani Alhaji mai suna Muhd Rabiu ya bayyana takaici game da wannan yanayi du sauke ciki.
To Amma Alhaji Lawan Sulaiman, janar manaja mai kula da aikace aikacen kamfanin na Azman ya alakanta lamarin da tangardar da jirgin na su ya samu a filin jirgin sama na Jidda a makon jiya.
Sai dai a cewarsa, tuni injiniyoyi suka shawo kan matsalar kuma zasu ci gaba da aikin jigilar fasinjojin su.
Yanzu kasa da makonni biyu ke nan suka rage kafin kammala umarar azumin watan Ramadana ta bana, domin kuwa nan kwanaki 10 masu zuwa ne ake sa ran karkare ibadar azumin watan na Ramadana.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahin Kwari: